Home

Music

Video

Kanny

ADAM A. ZANGO YAYI KIRA DA KAKKAUSAN MURYA

Fitaccen Jarumi Adam A. Zango


Daga Abu Fu'ad

Shahararren mawaki kuma Fitaccen Jarumi Adam A. Zango a makon daya gabata yayi kira ga kakkausan murya mai kama da harshen damo, inda wasu suke ganin kalaman yayi sune ga ƴan kallo masu sukan su ko kuma ga takwarorinsa ƴan fim. Inda yake cewa "Dafarko dai ina son in wayarwa jama'a da sauran abokai na kai, ko kuma in fahimtar dasu akan rubutun da nayi daga jiya zuwa yau, babu wanda ya zageni ko kuma yayi min wani abu ko yayi min laifi daya sa na fito nake irin waɗannan magagganu, amman abun da nake so kusani akwai wani abu wanda yake faruwa wanda ku baku sani ba, na farko wanda yake kallona fina-finai bai sanni ba don haka dole ya dunga samun shakku akan irin abubuwan da ake cewa zango zango, baya ku da kuke Najeriya haka suma wanda suke tsallaken Najeriya ma'ana African countries kenan irin su Nijar, Ghana, Kamaru, Gabon ko wata ƙasa ina iya inje in shiga inshaa Allahu sai anyi min tambayan shekara goma akan abunda akace Adamu Zango yayi na wannan shekarun, sannan in faɗa da baki na ince kaza gaskiya ne kaza ba gaskiya bane, sannan masoyana su yarda da abinda nake faɗa sunji na gasgata sannan sunji na ƙaryata. Shi mutunci da kuke gani a duniya ake kareshi, inda ka kare mutuncinka ka rasu shine zai cigaba da bibiyan ƴaƴanka in kuma baka kare mutuncika ba ka rasu inshaa Allahu zai cigaba da bibiyan ƴaƴanka walau sharri ko Alkhairi sauran abinda ka aikata wannan ya rage kai da mahaliccinka." Ya dai fitar da faifan bidiyo har kusan kala bakwai , a wani bidiyon kuma ya ya ci gaba da cewa " Mayan malamai da Masu sarautuma ana masu irin wannan kage ko kuma a faɗi abinda basu ba faɗa har sai ta kaiga sun fito sun kare kansu".
Duk waɗannan kalamai ya faɗa su ne a wasu bidiyo har 7 daya fitar a shafin sa na Instagram. Kafin sanya wannan bidiyo dai ya sanya wannan rubutun, wanda wasu da dama suke ganin kaman dasu yake. Ga bayanin daya fara na farko.






Wannan bidiyo dai ya ɗauki hankalin ƴan kallo da dama, inda su kai ta mai da tasu bahasi akai, ganin haka ana mu zaton ya sa jarumin ya cire wannan bidiyo a washe gari. A wannan watsn dai masoyansa da masu sha'awar ganin fina-finan sa da wakoki suna jiran ganin fim ɗinsa mai suna GAMDAKATAR da kuma faifan bidiyonsa mai suna MAI LAYA wanda jarumin yayi akawarin fitar dasu a wannan watan na Nuwanba.



Share this



Fb tt wp ig
Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team