Home

Music

Video

Kanny

AURE NE A GABA NA - FATI S.U

Fati Garba S.U

Sharfuddeen Baba

Fitacciyar jarumar wasannin fina-finan Hausa na Kannywood Fati S.U ta bayyana cewa  yanzu  ita
babban  burin ta a rayuwa shi ne aure sunnar Manzon Allah (SAW), kamar dai yadda ta shaidawa majiyar mu a cikin wata tattaunawa  ta musamman da tayi da ita.  Jarumar ta kuma bayyana cewa ita  tunda ta taso a rayuwar ta tana da matuƙar sha’awar yin wasan fim ɗin Hausa, amma ba ta samu damar cika burin nata ba sai yan shekarun nan bayan da ta haɗu da Adam A. Zango dake matsayin Uba gidanta a yanzu. Saboda haka ta ce a yanzu babban burin na shi ne aure, inji Fati Garba.


Jaruma Fati S.U 

Majiyar ta ƙara da cewa jarumar da yanzu haka ta ke gudanar da shirin nan na bautar ƙasa ta shaidawa majiyar ta mu cewar babban abun alfahari ne a gare ta yanzu yadda ta ke jerawa da kafaɗa da kafaɗa da shahararrun jaruman Kannywood ɗin wajen sana’ar su. Da aka tambayeta da game da jaruman da su ka fi bata sha’awa, sai jarumar ta ce tana da wanda ta ke so a harkar fim ɗin a yanzu haka amma ba zata ayyana shi ba sai nan gaba, amma cikin Jarumai mata ta fi son A’isha Aliyu Tsamiya.


Jaruma Aisha Tsamiya

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team