Home

Music

Video

Kanny

Ba zai yiwu Atiku ya ba Buhari kashi a shekara ta 2019 ba – inji shugaban APC

- Shugaban jam’iyyar APC ya ce ba zai yiwu Atiku ya kada shugaba Buhari a shekara ta 2019 ba
- Shugaban ya bayyana cewa ficewar Atiku Abubakar daga jam’iyya mai mulki ba abin mamaki ba ne
- Oyegun ya ce akwai alamomin da suka nuna kusan watanni 18 da suka wuce cewa Atiku zai bar jam'iyyar
Shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Cif John Oyegun, ya ce ba zai yiwu tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kada shugaban Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019 ba.
Shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Cif John Oyegun
Oyegun ya ce, '' Amma me ya sa mutane suke ta mamakin cewa ya bar jam’iyyar? Ba zan iya fahimta ba. Fiye da watanni 12 zuwa 18 da suka gabata, ya bayyana cewa zai fice. Abin da ba a sani ba shine yadda da kuma lokacin da zai sauya sheka”.
"Ga mataimakin shugaban kasa Atiku, a shekarunsa, ko dai a yanzu ko kuma har abada saboda idan shugaba Buhari ya zarce karo na biyu, wannan zai kasance shekaru 8. Akwai yiwuwar shugabanci zai koma yankin kudancin kasar”.
“Wannan wani shekaru 8 ke nan. Don haka, karshen wasa ke nan ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Ko dai yanzu ko kuma ya manta da shugabancin Najeriya har abada. wannan wani abu ne da muka sani tun tuni”

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team