- Tayi hakan ne ta hanyar rera wakar fim din a shafinta na Instagram
- Zango yayi matukar yaba wa bajintar ta
Fittaciyyar jarumar nan dake wasa a fina-finan Hausa, Faati Washa ta shiga layin dubban masoyan jarumin jarumai Adam Zango wajen tallata sabon fim dinsa da ya kusa fitowa kasuwa wato ‘Gwaska’.
Jarumar ta rera wakar cikin kwarewa ka ce it ace ta rubuta shi. Fati ta nuna bajintar nata ne a wani bidiyo da ta yi sannan ta wallafa a shafinta na Instagram.
Adam Zango ya yaba da bajintar Fati Washa wajen rera wakar Gwaska
Ta faro wakar daga farko har karshe inda har shi kansa Zango da ya shirya fim din sai da ya yaba.
Gwaska dai fim ne da ba ataba irin sa ba a farfajiyar Kannywood, saboda tsara shi da akayi da kuma irin abubuwan da akayi a fim din na gani na fada.
Zango ya sanar cewa zai gana da masoyan sa na Kano da ya hada da mata 15 maza 15 da suka fafata a gasar wakar fim din da ya sa a yi domin nuna wa kowa cewa alkawarin da ya dauka zai cika shi.




