Daga Abban Fu'ad, Kaduna, Najeriya.
A kullum masana'artar fim kar bunkasa take ta ko ina, kama daga yadda ake tsara fim ko shiryawa, haka zalika irin kayan da ake amfani dasu da kuma yadda zakaga matasa maza da mata nata tururuwa dan ganin sun bada tasu gudunmawar a cikin masana'arta.
Halima Ibrahim na ɗaya daga cikin sabbin jarumai mata data shigo da kafar dama domin bada ta ta gudunmawar a cikin masana'antar, inda tayi warwara kama daga tarihinta har zuwa yadda ta tsinci kanta a cikin masana'antar shirya fina-finai, da kuma irin rawar data taka acikin fina-finan data fito, wanda take saran nan bada jimawaba tana iya karɓe masana'antar ta zama gwarzuwar jarumar shekara a hira ta musamman da Abban Fu'ad.
Ganin yadda labarin fim ɗin ya karaɗe farfajiyar shirya fina-finan Hausa da kuma wasu daga cikin ƴan kallo wanda suka daɗe suna jiran sabɓin fina-finai daga kamfanin Iyantama multimedia, sai kuma ga labarin yadda ita sabuwar jarumar ta taka rawar gani, yasa Abban Fu'ad ya lalubota. Ga dai yadda hiran nasu ya kasance.
Jarumi Sadiq Sani Sadiq, Sabuwar Jaruma Halima Ibrahim da kuma Jarumi Hamisu Iyantama a lokacin ɗaukar fim ɗin Uwar Bari.
Kannywoodtoday: Zamu so muji sunanki?
Halima: sunana Halima Ibrahim, Ni asalina ƴa Jahar Adamawa ce amman an haifeni a garin Kano, inda anan nayi karatuna na Firamari da Sakandare, Sannan naje Jami'ar Kimiya da Fasaha dake Fagge duk a Jahar Kano, inda na karanta Nazarin Kwamfuta wato (Computer Science) a turance.
Kannywoodtoday: A matsayin na wacce ta karanta Nazarin Kwamfuta, Meya baki sha'awar shigowa harkar fim, gashi karatunki bai haɗa layi da fim ba?
Halima: Na daɗe ina sha'awar harkar fim, ince ma tun ina ƙarama nake sha'awar wannan harkar amman ganin ba zai yiwu a wanchan lokacin ba na barma zuciya, sai bayan na gama makaranta sannan na bayyana ma iyayena ra'ayina akan harkar fim, Alhamdulillah, da yake iyayena masu fahimtane kuma masu son abinda ƴaƴansu ke so kamar yadda muma muke koƙarin yi masu dukkannin wani abu da suke so da zai faranta masu rai, sai suka amince min tare dayi mani addu'a akai in alheri ne Allah ya bada sa'a gami da jan kunne akai.
Kannywoodtoday: Tun yaushe kika samu daman shigowa wannan harkar?
Halima: Aƙalla nakai wata Uku, kuma ina shigowa aka amsheni hannu biyu.
Halima Ibrahim
Kannywoodtoday: Kawo yanzu aƙalla kinyi fina-finai nawa?
Halima: Nakanyi ma Allah godiya domin a watan dana shigo Allah ya haɗani da mutanen arziki, inda suke kokarin gani sun taimakamin don cimma burina a wannan masana'antar, da shigowata inda akamin fim mai suna Rabu Da Maza wanda wannan fim kamar gwaji ne akayi akaina inda nine maitaimakiyar Jarumar fim ɗin. Sai wanda Sadiq Sani Sadiq shine jarumin fim ɗin, inda ake kasheshi a cikin fim ɗin mai suna Uwar Bari na Kamfanin Hamisu Iyantama, wato Iyantama Multi media wanda Sir Hafiz Bello ya bada Umarni sannan nice naja wannan fim ɗin, sannan akwai wasu guda shidda wanda ban san sunan su ba tukunna, amman duk a cikin su nafi ji da Uwar Bari wanda ina sa ran masu kallo kansu zasu soshi kuma dashi nima zan kara taka wani matsayi a masana'antar.
Kannywoodtoday: To me yaja hankalinki kikafi san fim ɗin Uwar Bari?
Halima: Wato Abban Fu'ad Uwar Bari fim ne wanda labarinsa ya banbanta da fina-finan dana kalla a baya, domin labarin fim ɗin akwai abubuwa da dama wanda ƴan kallo zasu Ilmanta dashi musamman a zamanta kewar rayu sannan ga darrusa acikin fim ɗin da dama, domin fim ne dake nuna yadda zaurawa sukayi yawa a society ɗin muna yanzu, kar dai ace na kuzuzuta fim ɗin dan nice a ciki, amman masu kallo su jira su gani zasu so fim ɗin sosai, kuma nasan zasu soni aciki yadda na bada tawa gudunmawar dan ganin an samu abinda ake so a ciki.
Kannywoodtoday: Wasu kan ɗauki masana'antar fim amatsayin guri na gurɓata tarbiya ba gun gyara tarbiya ba ke aya kika kalli masana'antar?
Halima: Dafarko ina godema Allah da irin iyayen da ya bani domin ita tarbiya tun daga gida ake samunta, sannan kuma dana shigo harkan fim ya haɗani da iyayen gida nagari Im so greetful about that, domin duk inda kaga mutumin banza daman tun a gida haka yake, to gaskiya masana'antar fim a guna wata sabuwar Jami'a ce ta inda zaka haɗu da mutane daban daban kuma kuyi rayuwa a tare har lokacin da Allah ya raba ta aure ko mutuwa, zan ma iya cema tafi rayuwar Jami'a kuma kamar yadda na faɗa ni dai nayi sa'a domin hannu nagari na faɗa kuma ina rokon Allah dakar ya haɗani da gurɓatantu a wannan harkar. Saboda haka masana'antar fim ba gun bata tarbiya bane sai dai ta gyara rayuwarka ta ɗauraka akan hanyar data dace.
Kannywoodtoday: Akasari sabbin jarumai musamman mata in sun shigo sai kiga burin su shine su fito a cikin fim da wane da wane, ko kema kina da wannan ra'ayin?
Halima: Gaskiya ne wannan, nima ina da wannan ra'ayin duk da babu wanda in aiki ya haɗani dashi zanyi iya kokarina ta yadda zan burge ƴan kallo, amman a burina daman na fara aiki da Ali Nuhu, Adam Zango ko Sadiq Sani Sadiq, sai kuma Allah ya amsamin wannan addu'ar tawa inda na fara da Sadiq Sani Sadiq suma kuma nasan nan bada jimawa ba zan fito a fim dasu kodan irin kwazona a fim.
Kannywoodtoday: Ganin yadda mata keda yawa kuma gasa a tsakanin su tai yawa wani matsayi kike saran kaiwa?
Halima: (Sai ta danyi dariya) Gaskiya yadda na yarda da kaina da kuma irin rawar danaga na taka a cikin fina-finan dana fito gaskiya banganin kowace jaruma a gabana, domin gogaggun ma'aikata nayi aiki dasu musamman uban tafiyar Sir Hafiz Bello sanin kowa ne yasan aikinsa a harkan fim musamman bada umarni to kaga ni horansa ce, saboda haka ban cire tsammanin a shekaran nan da fina-finai na zasu fita ban samu award ɗin sabuwar jarumar shekara ba, kuma ni har award ɗin gwarzuwar jarumar shekarar inaga zan iya samun duka duk da award bashine a gabana ba, kama zuciyar ƴan kallo shine burina da kuma biya masu bukatar su a cikin fim.
Kannywoodtoday: Ganin yadda mata da maza kullum tururuwa sukeyi a cikin wannan masana'antar, wani kira zakiyi ga masu shirya fina-finai akan karɓar sabbin fuska kuma a daina ware ƴar mowa da ƴar bora?
Halima: Dafarko kirana ga su sabbin jaruman dake neman dama musamman mata, sai kin rike darajarki ki kuma kama kanki domin in kika ballagazar da kanki babu wanda zai ɗaukeki da daraja ballantana ya zuba dukiyarsa akanki, haka suma mazan, sannan babban kirana ga producers shine sai kun chanja daga in ba wane ba ni bazanyi ba dan ko nayi asara zanyi, riba da faɗuwa dukka Allah ke badawa sai kun sa tawakkali da sanin Allah a ranku sannan zaku cigaba kuma masana'antar takara progressing, kuma baiwa sabbin jarumai dama ku zai taimakamawa domin basai kun dau lokacin jiran wance ba ko wane akoda yaushe ba. Sannan ku kuma jaruman da muka tadda sai kunyi hakuri damu kun rugumemu hannu biyu kaman ƴan uwa haka muma sabbin mu rungumeku kaman ƴan uwa sannan zamu cigaba, domin Allah kaɗai yasan dalilin dayasa ya haɗa mu agu ɗaya dan yin sana'a tare. Sai kuma mun cire hassada akan juna domin ita hassada ba inda take kai mutum sai ci baya, inda mutum yayi abin yabawa ka yaba mai inda ya saɓa ka mai gyara amatsayinka na babba koda ko ya girmeka domin kai yasamu a ciki, abida kasani kafin ya sani sai ya ɗauke shi lokaci mai yawa kafin ya sani. Sannan biyayya na da matukar muhimmanci a rayuwa mu mutunta nagaba damu mu masu biyayya sai muma na baya in sunzo su mutuntamu su mana biyayya fiye da yadda mukayi a baya sai kaga anci ba baki ɗaya. Kuma kar mu manta duk abinda mukeyi duniya na kallon mu kuma haka za'ata ya yata abin kuma mu dawo muna jin haushi koda nasin wanda Hausawa sukace keyace. Allah ya haɗa kawunan mu duk wata fitina Allah ya tsaremu da tsarewarsa.
Halima Uwar Bari
Kannywoodtoday: Daga karshe wani albishir zakima ƴan kallo akan ganin irin rawar da kika taka dan jiran fina-finan da kika fito?
Halima: Kar dai ace na cika baki dayawa amman su jira fim ɗin Uwar Bari wanda kamfanin Iyantama multimedia ya shirya sannan babban yayana Sir Hafiz Bello ya bada umarni, da kansu ƴan kallo zasu warware zare da abawa gun isar da sakon da ake bukata.
Kannywoodtoday: Mun gode, muna fatan Allah ya bada sa'a.
Halima: Nike da godiya da wannan hiran da akayi dani, Amin na kuma gode da wannan addu'an.




