Home

Music

Video

Kanny

NAFISA ABDULLAHI TA ZAMA JAKAƊIYAR LEAƊERSHIP A YAU

Jaruma Nafisa Abdullahi kuma Jakadiyar Leadership A Yau.

Dag Sharfuddeen Baba, Kano, Najeriya.

A Larabar data gaba rukunin kamfanin dake buga Jaridun Leadership A Yau suka kammala shirye-shirye tsakanin kamafanin da fitacciyar Jarumar Nafisa Abdullahi wacce tayi suna  wajen fita  a matsayin  mai haƙuri a fina-finan Hausa, inda ta zama Jakadiyar Leadership  A Yau.

Bayan ƙulla wannan yarjejeniya Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, da farko  dai ina miƙa godiya  ta ga kamfanin Leadership A  Yau, na yi matuƙar farin cikin kasancewa ni ce Jakadiyar Leadership A Yau ta farko.
Yadda aka ɗauke ni da muhimmanci  ne ya sa har ake so a mayar da ni Jakadiyar Jaridar Leadership A Yau.


Nafisa A lokacin da aka kaddamar da ita a matsayin Jakadiyar Leardership A Yau.

Duk da tarin Jaruman da suke Nijeriya, an ɗauke ni, ni ce ta farko wanda aka ba ta wannan babban matsayi. 

Don haka ina matuƙar farin ciki. Ta ci gaba da bayyana cewa, lalle zan bada ƙarfin gwiwa don in ga wannan alaƙa tamu ta ɗore fiye da yadda muke tunani za mu samu. 

Jaruma Nafisa Abdullahi  ba ta kammala jawabinta ba sai da yi kira ga al’umma, tace  ina kira ga jama’ar gida Nijeriya  dama ƙasashen waje, su rinƙa karanta Jaridar Leadership A Yau , domin za su rinƙa ganin abubuwa daban –daban waɗanda za su ilimantar, faɗakarwa da kuma nishaɗantar da su.

Share this



Fb tt wp ig
Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team