Home

Music

Video

Kanny

BAN JI DADIN SATAR FITA BA By Duniyarhausa














kofa nayi

Duk da mijina mutum ne mai tsananin biya mini bukatuna, da kokarin sauke nauyin da ke kansa, sam zaben sa da siyayyarsa ba su gamsar da ni, hakan ya sanya lokuta da dama muke samun sabani idan ya kawo mini kaya ko na yarana, tun yana fishi idan na kushe har ya saba, zai yi abin sa gaba gadi ko na yaba ko na kushe bai dame shi ba.
A wannan sallar ma haka ya yo siyayyar kayan sallar sa, bai shigo daki na ba sai ya wuce dakin sa ya kira 'ya'yansa ya fara raba musu, sai ihu da murna na jiyo na yara ana ta gwada kaya, na shiga dakin na tsaya ina kallon kayan, rai na ya baci don sam ba su yi mini ba, na sami guri na zauna nace.
'Haba Malam yaya zaka si yo musu wannan kayan, bayan kasan sarai kayan suwaga ake yayi, ni kam wallahi ba su burge ni ba sam.'
ya daga kai ya kalle ni ransa a bace kamar zai yi magana, amman sai ya fasa ya ci gaba da sanyawa yaro na na goye kayan sa.
Na kara tabe fuska na ce 'Yanzu kuma nawa-nawa ka siyo su? nasan wallahi an cuce ka, da ka bani na siyo musu ka gwammace ka je a cuce ka ko?
Sai a sannan yayi magana. 'Da na yadda matata ta shiga wannan turereniyar ta kofar wambai gwara a cuce ni ko nawa ne, ke yanzu Salma idan nace ki shiga wannan turmtsutsun sai ki shiga?
Bai bari na yi magana ba yaci gaba 'Duk abin da naga ya dace da 'ya'yana shi zan sai musu, sai kije ki yi ta surutun ki.'
daga wannan maganar bai kara cewa komai ba ya bar ni ina ta mita, ina fadin 'Idan da gaske ne, ai sai a bani kudi kafin azimin na siyo, ko kuma ka dauke ni a mota mu tafi Jifatu ko Sahad mu siya.' shi dai bai kula ni ba.
Kwana na yi ina sakawa da kwancewa, don bazan taba yadda ace 'ya'ya na ba su sanya kayan suwaga ba, da gari yayi sha lokacin malam ya tafi kasuwa na aika babban da na nace maza ya garzaya gidan Ladi mai da shi ya ce ta ba ni dauka ta, daman na gaya mata siyayyar sallah zan yi wa yara.
Kafin kace kwabo Adamu ya dawo da kudin dashin kulle a leda, na kwance na lissafa dubu tara ne da dari biyar
Ta dauki karan dashi naba adamu yakai nagoya karamin dana Aminu muka fita na tsari adaidaita sahu nahau.
BAN JI
DADIN SATAR FITA BA! 2
Kwatakwata ban kula da akwai hadari a garin ba sai da muka fara tafiya, faduwar gabana ta karu lokacin da aka fara yayyafi, kafin mu isa kasuwar Wambai an tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya, hakan ya sanya duk na gigice na rude, kamar na ce ya juya na koma gida, amman wata zuciyar tana sanar da ni gwara na je, tunda gobe na sallah, idan ban je yau ba shike nan, haka muka ci gaba da tafiya har muka isa, na yi zaune cikin motar ina tinanin yanda zan fita cikin ruwa, ina ganin mata tsamo-tsamo cikin ruwa suna ta ciniki ba su damu da ruwan da ke dukan su ba kamar a garin Legas, sai da mai Adaidaita din yace Hajiya ki fita mana, sannan na fita, da fari na fake jikin wani gini da na ga an rubuta Gidan Kurfi, amman ganin ruwan ba shi da niyyar daukewa, ga kuma ganin mata suna ta kaiwa da komowa a ciki ya sanya na fice kawai na kutsa cikin kasuwar, yawan mata da turereniyar da ake yi ya sanya ba ka iya ganin kayan ta dadin rai, hakan ya sanya na yi ta zaga ye ruwa yana dukan mu ni da Aminu.
Haka muka jike jagab, tun Aminu yana kuka har ya gaji ya daina, domin babu inda zan fake na bashi ya sha, fatana na kammala siyayyar mu koma gida, a wani shago na hango kayan da nake so na shiga na fara ciniki, ruwa yana diga daga jikina, muka kammala cini ki na zuge jaka zan dauki kudi suka ce neme mu inda kika ajiye, hankalina ya tashi matuka, duk wani loko na jakar nan na duba amman ban ga kudin nan ba, tabbas an sace mini, bana raba daya biyu wata matace data dinga bina ta kwashe kudin nan, bakin ciki ya cika ni kamar na fashe da kuka, haka na juya da zummar barin shagon, sai wani mutum yace mini.
'Hajiya ai dan da ke bayan ki ya rasu.'
Tamkar ya daba mini wuka a kirji, na kwanto Aminu da sauri jiki na yana rawa, ai kuwa Aminu ya rasu, na rasa abin da zan yi sai na fashe da kuka, jama'a suka taru akai na kowa da abin da yake fada, jikina ya dinga rawa na rasa abin yi ma.
BAN JI DADIN SATAR FITA BA 3
Kuka nake kamar raina zai fita lokacin dana tabbatar Aminu ya rasu, jama'a suka taru a kaina ana ta bani hakuri, wasu kuma suna Allah ya kara, da kyar na iya mikewa don tafiya gida, amman sai na tina bani da ko kwandalar komowa gidan, nan na fara rokon jama'a a taimaka mini da kudin komowa gida, aka hada mini dari biyu da tamanin na kama hanyar gida, da kyar bayan tsayuwa kamar ta awa guda na sami motar da zata kai ni unguwar mu, amman ban ce musu gawa ce a bayana ba, haka na nufi gida ina share kwallah, ina addu'ar Allah ya sanya baban su Adamu bai da wo ba, naje na kwantar da Aminu na masa waya.
Amman abin da ya bani tsoro bai wuce jaje da wasu suka fara mini bayan na sauka daga Adaidaitan ba kafin na karasa gida, wanda yayi mini na farko ban kula ba sai da wani ya kara mini yana cewa.
'Ashe haka wannan abin ya faru, to Allah ya kiyaye gaba.'
da sauri na ce masa ' wai me ya faru ne?
Ya kalle ni da mamaki yace 'Ko ba kya nan aka yi gobarar ne...
A firgice nace 'Gobara a ina kuma...na shiga uku...ba dai a gidan mu ba....
Kafin ya bani amsa na nufi gidan a firgice, tun daga soro na fara jiyo kauri abin da ya sanya na shiga a sukwane, sai na hango kicin din mu ya kone kurmus, na fasa ihu a firgice ina kwalawa yaran kira, Azima ce ta fara fitowa daga cikin daki idon ta ya kada yayi ja, cikin karaji nace mata ina Adamu.
Sai ta fashe da kuka tana fadin 'Umma Adamu ya kone a hannu da kafarsa, bayan kin fita ba dadewa ya shiga ya kunna gaskuka, ban san yaya aka yi ba kawai sai ihunsa da kamawar wuta muka ji, na fita da gudu ina ihu awaje, dai-dai lokacin Baba ya dawo kawo cefanan Sallah ya shigo gidan a gigice da kyar suka kashe wutar bayan an janyo Adamu, yanzu suna Asibiti.
Na kara fashewa da kuka ina fadin 'Na shiga uku ban ji dadin satar fitar nan ba, wayyo Allah na.'
daidai lokacin baban su ya dawo, ya kalle ni sama da kasa bai ce mini komai ba, ya shige dakin sa yana hada kaya da alama kwantar da su aka yi, na shiga dakin ina kuka nace ma
na shiga dakin ina kuka nace masa Aminu ya rasu, ya jima yana kallo na sai naga idon sa yana zubda hawaye, ya fita ya tsaya yana kallon gawar Aminu dana kwantar sannan ya fita waje, ba a jima ba ya dawo da likkafani da mutane su ka yiwa Aminu wanka suka kai shi, bayan sun dawo ne, ya bani takadda da saki biyu, yace na bar masa gidan sa.
Bai waigo ni ba har yau, ga bakin cikin saki gana mutuwar dana, ga na konewar Adamu, tabbas ina cikin tsaka mai wuya, ku taimaka mini da addu'a 'yan'uwa.shin ahaka mata zasu taimaka wurin zaman aure wlh mata mu kiyaye
Zinariya

Share this



Fb tt wp ig
Copyright © 2018 - 2025 Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team