Home

Music

Video

Kanny

Dalilan dake kawo Rugujewar Soyayyar Ango Da Amarya Bayan Aure By Duniyarhausa




Ango da amarya sau tari soyayyarsu tana mutuwa bayan aure, ta yanda kulawa ta kan yi karanci da kuma damuwa da juna ya ragu idan aka yi la’akari da lokacin da ba a yi aure ba,

za ka ga kusan kullum ana matse da juna, marmarin kallon juna ake yi ba a son rabuwa duk lokacin da aka hadu to amma abin da ya fi bawa mutane mamaki shi ne lokacin da aka shaku kuma ya zama kullum ana tare sai ka ga ana yiwa juna kallon raini musamman ango an fi samun raunin soyayya a wajensa.

Amma kuma manyan dalilai suna nuna laifin ya fi fitowa daga wajen mace shi.

 Wannan ya sa na ga ya dace a wannan makon in kawo wannan darasi da ya kamata amarya ta lura da su domin karamin kuskure zai iya hana ki farin ciki tsawon rayuwarki.

 Wacce Irin Soyayya Kuka Yi Kafin Auranku? Soyayya da ‘yan mata suke yi a yanzu akwai kuskure sosai a cikin ta, ta yanda mace za ta bawa namiji jikinta tamkar mijinta koda be sadu da ita ba to zai zama kullum idan ya ji sha’awa ita za ta rika gamsar da shi, wannan kuma ba karamin ruguza rayuwar aure yake yi ba duk wata soyayya da saurayi yake miki ko kuma wanda kike yi masa to kada ki sake ko hannunki ya rike koda kuwa zai iya kawo rabuwarku.

Hakan shi ne zai sa ki yi mutunci tare da kima wanda da dama wasu amare suka rasa a wajen angwayensu amma koda wasa idan kika biyewa soyayya tare da bin son zuciyarki to tabbas ki shirya fuskantar wulakanci bayan aurenku. Kin Je Gidan Aure Da Budurcinki? Wasu amare tun daren farko ango yake fara daure mata fuska saboda ya ji ta sabani yanda ya ji ana fada koda kuwa ba shi da ilimi a kan abin to zai yi wahala a ce bai san mene ne budurciba.

A baya yana kallon ki da kima yana ganin ya yi sa’ar aure to amma a wanna daren zai fara zarginki koda kuwa da shi kika bata budurcin naki zai yi tsammani ba shi kadai ya yi mu’amala dake ba kuma koda kuskuren fahimta ya yi to wannan zai sa ya yi ta kallon ki da abun, matsala ta yi ta girmama memakon a baya kuna mararin juna yanzu sai ki ga baya son zama kusa dake baya hira dake, a wani lokaci ma shi ne musabbabin rabuwarsu. Shi ya sa idan kina son kima to kada ki yi wasa da budurcinki, sha’awa ta lokaci kadan ce daga kin yi hakuri za ta wuce amma bakin cikin aure ba ya wucewa.

 Mummunan yanayi ne wanda ba zai bar zuciyarki ba sai dai mutuwa ta raba ki da shi.

Don haka mutuncinki a gidan miji tun kina budurwa za ki same shi ta hanyar kyamar duk wata mu’amala da za ta saka namiji ya taba jikinki.

Rashin Nuna Wa Ango Tausayi Sau da dama za ka ga ana soyayya sosai amma da zaran an zo hidimar biki sai ka ga amarya tana matsa wa ango ya yi abin da ba ya dashi, haka za ka ga ango yana ta kashe kudi a kan abin da ba farilla ba, wannan ba ya bata wa ango rai sai bayan biki domin wani bashin kudin zai yi don ya faranta miki rai, zai rinka tuna abun yana ganin ki a matsayin marar tausayi ba shi kike so ba dan haka dole amarya sai kin yi hakuri kin bar abun da ba dole ba don tausaya wa angonki.

 Wadannan abubuwan suna kawo rugujewar soyayya bayan an yi aure, don haka mata da maza sai a kula sosai, kar a bari soyayyarmu ta ruguje bayan mun yi aure ba da jimawa ba, domin wannan babban abin kunya ne tare da kawo bakin ciki mara misaltuwa a rayuwa

Share this



Fb tt wp ig
Copyright © 2018 - 2025 Powered by DuniyarHausa and Developed By DuniyarHausa Web team