Fitaccen malamin addinin ya samu damar fita zuwa kasar Indiya ranar Litinin bayan wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belinsa domin a duba lafiyarsa da matarsa, kamar yadda lauyoyinsu suka bukata.
A wani jawabi da babban sakataren ma'aikatar yada labarai da al'adu, Grace Isu Gekpe, ya fitar, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnati tayi watsi da wannan bukata ta Zakzaky saboda an bashi damar fita ne domin a duba lafiyarsa, ba don yawon bude ido ba.
"Zakzaky ya nemi a bashi izinin ya yi yawo yadda yake so da kuma bukatar ya sauka a wani babban Otal tare da karbar bakuncin duk wanda yake so, sakamakon wuce wa da shi zuwa asibitin da za a kwantar da shi.
"Ya nemi hukumomin kasar Indiya su taimake shi domin a janye masa jami'an tsaron da aka hada su tafiya tare daga Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa tun a kasar Dubai Zakzaky ya fara nuna yana wata nifaka a kan yarjejeniyar da aka kulla da shi kafin ya samu belin fita daga Najeriya.
Sanarwar ta cigaba da cewa; "ya nemi a bar shi ya zabi likitocin da za ai masa aiki a asibitin da aka kai shi, wanda yin hakan ya saba da dokar asibitin da kuma na aikin lafiya.
"Wannan bukatar da ya bijiro da ita ta kara kawo tsaiko a kan lokacin da ya kamata a fara yi masa aikin da ya kamata. Cikin fushi hukumomin asibitin suka hakura ya zabi likitocin da zasu duba shi kuma a asibitinsu.
"Ita kan ta kasar Indiya ta ki amince wa da bukatunsa saboda bata bukatar ya yi amfani kasar ta domin harkokin kungi yarsa.
"A saboda haka ne ya fito yana korafin cewa an saka shi cikin mawuyacin hali a kasar Indiya, wanda yafi na Najeriya muni."